Yadda Ta Kaya A Wurin Taron Karawa Juna Sani Wanda NUJ Da NITDA Suka Shirya A Jigawa

0 79

Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar jigawa Alhaji Sunusi Hussaini Madobi ya bayyana makasudin taron nasu da nufin wayar da kan abokan aiki dangane da matsalolin da labaran karya da kyama ke dashi a cikin al’umma.

Shugaban hukumar NITDA Alhaji Kashifu Inuwa Abdullahi, lokacin da yake gabatar da maqala akan muhimmancin Fasahar sadarwa ta zamani (ICT) tare da matsalolin da take haifarwa a kasashe masu tasowa a fannin aikin Jarida, ya bayyana cewa zasu hada karfi wajen samar da ingantattun bayanai a bangaren jarida a kasar nan.

Shi kuwa Alhaji Lawan Muhammad Danzomo  kwamashinan ma’aikatar ilimi ta jihar jigawa kira yayi ga masu amfani da kafafen sadarwa na zamani da na sada zumunta da sauransu da su rinka amfani da kafafen ta hanyar da ta dace, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki daya.

A nata bangaren shugabar jami’ar tarraya dake Dutse Farfesa Fatima Batulu Mukhtar ta bayyana jin dadin ta game da yadda taron ya gudana, inda tayi kira ga al’umma da suci gaba da bawa ‘yan jaridu goyan bayan daya dace a kokarinsu na samar da sahihan labarai a cikin al’umma. 

Da yawa cikin wadanda suka tattauna a taron na karawa juna sani, sun mayar da hankali ne kan matsalolin da fannin jarida ke fuskanta sakamakon rashin kwarewa da masu amfani da kafafen sadarwa na zamani ke dashi, ta yadda suke amfani da kafar wajen yada labaran karya da kyama a tsakanin al’umma.

A don haka ne da yake jawabi a yayin a tattaunawarsu da wakilin Gidan Rediyon Sawaba jiya a birnin Dutse, Dan masanin Dutse Adamu Aliyu Kiyawa ya shawarci yan jarida da su koyi dabi’ar yawan nazari da bincike-bincike tare da tabbatar da labari kafin wallafa shi, kana su ma mutane su rika kokarin tabbatar da sahihancin labarai kafin yada shi a kafar sadarwar zamani.

Daga Faruk Ahmad

Leave a Reply

%d bloggers like this: