Nijeriya Ta Dauki Matakin Rigakafi Kan Cutar Corona Virus

0 136

Gwamnatin tarayya tace tana iyakokarinta dan ganin ta dakatar da yaduwar zazzabin cutar Lassa, wanda ya watsu a sassa daban-daban da ke fadin kasar nan tun shigowar wannan shekarar ta 2020.

Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin Ministan lafiya na kasa, Mr Osagie Ehanere, cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Ministan ya ce ma’aikatar lafiya, tana iya kokarinta wajen ganin ta dauki matakan dakile yaduwar cututtukan da suka bulla, da suka hada da kwayar cutar Corona virus da sauran cututtuka.

Ministan ya kara da cewa an kafa babban kwamatin da zai rika kulawa wajan tabbatar da cewa an dakile yaduwar cututtukan.

Kazalika ministan ya sanar da cewa a yanzu haka ma’aikatar lafiya ta kasa ta kaddamar da shiri a filayen sauka da tashin jiragen saman kasa da kasa da kuma kan iyakokin kasar nan domin hana kwayar cutar Corona virus shigowa cikin kasar nan.

Babban Darakta Mai kula da shirin Mr. Joshuwa Obasanya ya bayyana bukatar da ke akwai wajan ganin an dauki matakan dakile yaduwar cutar Lassa a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: