Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da shawagabannin majalisar dokoki kan kalubalen da Najeriya ke fusanta kan al’amuran tsaro jiya, a Abuja.
Yayinda suka amince da cewa za suyi iya yinsu wajen dakile matsalar.
Kakakin majalisar tarrayya sanata Ahmad Lawan, ya tabbatar a zauren taron, a ganawar da su kayi jiya a fadar Shugaban kasa kan matakan da za’abi wajen dakile matsalar.
Yace sun gana da Shugaba Buhari kan al’amuran tsaro da kuma wasu al’amuran gwamnati.
“Magance matsalar tsaro yana bukatar hadin kan manyan Jami’an gwamnati,” A cewar kakakin majalisar.
Yakara da cewa Sun gudanar da muhawara a fannoni guda biyu na majalisun, kan abubuwan da suka shafi tsaro makon daya gabata, sannan aka cimma matsaya, kana suka gana da shugaban kasa, yadda za’a bullowa kalubalen.
Yace sun tattauna duk kalubalen dake fuskankar Najeriya a zamannasu, ya kara da cewa sun tattauna bukatar Karin kayan aiki ga dakarun tsaro na yan sanda da Jami’an farar hula don gudanar da aikinsu cikin nasara.
Kakakin majalisar ya kara da cewa, shubagan kasa Muhammadu Buhari zai yi aiki da majalisar tarayya wajen shawo kan matsalolin tsaro a najeriya.
“Ko shakka babu shugaban kasa yafi kowa damuwa da matsalolin tsaro, Don haka za muyi iya yinmu muga an wadata jami’an tsaro da kayan aiki Don su gudanar da aikinnasu.” inji kakakin majalisar.