Jami’an hakumar Hisbah ta jihar jigawa sun kama mutane 31 saboda ashararanci da rashin da’a

0 79

Jami’an hakumar Hisbah ta jihar jigawa, sun kama mutane 31 da suka hada da mata 25 bisa abin suka bayyana da aikata ashararanci da rashin da’a.

Kwamandan Hisbah na jihar Jigawa, Mallam Ibrahim Dahiru, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa, an kama wadanda ake zargin da misalin karfe 6 na safe bisa zarginsu da da yawon ta zubar da shan barasa.

wadanda ake zargin sun hada da mata 25 a karamar hukumar Kazaure.

A cewar an kama mutanen ne a wani samame da hukumar Hisbah ta kai mai taken “Ka girba abin da ka shuka”.

Ya ce an kama kwalabe 55 na barasa iri-iri, da lita 50 na barasa yar cikin gida wato “Burukutu” a yayin farmakin.

Ya kara da cewa an mika wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kama ga hakumar ‘yan sanda a yankin domin ci gaba da daukar mataki.

Haka kuma Dahiru ya yabawa mazauna jihar bisa goyon bayan da suke baiwa kungiyar.

A cikin Yuli 2021 ne, hukumar Hisba ta haramta amfani da giyar burkutu ta hanyar ‘yan kasuwa na zamani, masu shaguna, da a cikin tallace-tallace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: