Jami’in Kungiyar HAMAS yace a shirye kungiyar take ta saki dukkan sojojin Isra’ila da suka tsare

0 223

Wani babban jami’an kungiyar Hamas yace a shirye suke su saki dukkan sojojin Isra’ila da suke tsare da su, domin musayar fursunonin su Falasdinawa dake tsare a Isra’ila, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Tsohon Ministan lafiya a Gaza Bassem Naim yace kungiyar na tattaunawa domin duba yuyuwar tsawaita tsagaita wuta ta kwanaki 6 wacce ke kawo karshe a yau Alhamis, domin bada damar sakin mutanen da ake tsare da su.

Mayakan Gaza na rike da mutane 240 wanda suka kama a kudancin Isra’ila ranar 7 ga watan oktoba.

Yayin harin hukumomin Isra’ila sun ce an kashe musu mutane sama da 1,200 galibi fararen hula.

A nata martani, Israla’ila ta sha alwashin shafe Hamas daga doron kasa.

Kungiyar Hamas tace ta kashe Isra’ilawa sama da 15,000 mafiyawan su fararen hula. Kawo yanzu dai Fursunonin Isra’ila 60 Falasdinu ta saki, yayinda ita kuwa Isra’ila ta saki Falasdinawa 180 karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: