‘Yan bindiga sun halaka mutane 18 a hare-hare mabambanta da suka kai jihar Taraba

0 150

Manema labarai sun rawaito cewa Mafarauta 15 a lokacinda da suka tunkari ‘Yan bindiga a garin Maihula ranar Talata.

An rawaito cewa ‘Yan Bindiga kimanin 200 sun kain farmaki garin na Bali inda suka mamaye kauyen, amma duk da haka Mafarauta sun tunkari ‘yan bindigar.

‘Yan bindigar sun je garin ne dauke da muggan makamai inda suka kashe mazauna garin kimanin 15.

Shugaban kungiyar Mafarauta ta jihar Adamu Dantala, ta tabbatarwa manema labarai cewa maharan sun kashe mutane 15 cikin hadda wani dan kungiyar su.

Ya kuma kara da cewa ‘Yan bindigar sun yi kwantan bauna a yankin Dakka na karamar hukumar Bali, inda suka kashe mutane 3. Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar SP Usman kawo yanzu bai ce komai ba dangane da harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: