Jam’iyyar APC Reshen Jihar Gombe Ta Kori Sanata Muhammad Danjuma Goje Daga Jam’iyyar

0 68

A yau ne jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta kori Sanata Muhammad Danjuma Goje daga jam’iyyar bisa zargin cin zarafin jam’iyyar.
A watan da ya gabata ne jam’iyyar a matakin mazaba ta kafa kwamitin da zai binciki zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa da Sanatan ya yi a zaben 2023.
Da yake jawabi ga manema labarai a garin Kashere, shugaban jam’iyyar APC na mazabar, Tanimu Abdullahi, ya bayyana cewa jam’iyyar ta yanke shawarar korar Danjuma Goje ne bayan ta same shi da laifin yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Tanimu Abdullahi ya kara da cewa, ana kuma zargin Sanatan da kaurace wa duk wani rangadin yakin neman zabe na jam’iyyar a shiyyar sa ta Sanata, da mazabar dan wakilai ta Akko, da dan majalisar dokokin jiha da kuma na mazaba.
Shugaban jam’iyyar na mazabar ya kuma yi zargin cewa Sanata Danjuma Goje ya bayar da umarni karara ga magoya bayansa na yiwa jam’iyyar APC zagon kasa a jihar Gombe ta hanyar tabbatar da cewa shi kadai aka zaba a jam’iyyar APC tare da kokarin ganin an kayar da sauran ‘yan takarar APC a dukkan matakai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: