Hukumomi A Tunisiya Sun Hana Gudanar Da Taro A Dukkan Ofisoshin Jam’iyyar Adawa Ta Ennahda

0 80

Rahotanni daga Tunisiya na cewa hukumomi sun hana gudanar da taro a dukkan ofisoshin jam’iyyar adawa ta Ennahda, sa’o’i bayan ‘yan sanda sun tsare shugabanta.
Majiyar jam’iyyar Ennahda ta ce an kuma rufe hedikwatar kawancen jam’iyyar adawa ta Salvation Front.
A yammacin jiya ne aka kama shugaban jam’iyyar Ennahda Rached Ghannouchi a gidansa da ke Tunis babban birnin kasar.
An kuma bayar da rahoton cewa an tsare wasu fitattun jami’an Ennahda uku.
A bana dai an yi ta kame manyan jiga-jigan masu adawa da shugaba Kais Saied, wanda ya karbi cikakken ikon zartarwa kusan shekaru biyu da suka gabata.
A wani labarin kuma, Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisi ya tabbatar da cewa wasu sojojin Masar na cikin makwabciyar kasar Sudan amma ba su da hannu a fadan da ake yi.
Ya ce sun je wurin ne a wani shirin horaswa na hadin gwiwa ba tare da nuna bangaranci ba a rikicin da ake yi tsakanin rundunar sojin kasar da mayakan kungiyar RSF.

Leave a Reply

%d bloggers like this: