Uwar Jam’iyyar APC ta kasa ta turo kwamati mai wakilai 7 zuwa jihar Jigawa domin gudanar da zaben fidda gwani, tare da kaddamar da rabon kayayyakin zaben wakilai wato deliget.

A jawabinsa, jagoran kwamatin Malam Ibrahim Ahmed, ya ce sun zo jihar Jigawa ne domin gudanar da zaben wakilai da za su zabi ‘yan takara na jam’iyyar APC a fadin jiharnan.

Ya ce za’a gudanar da zaben ne ta hanyar zabe ko kuma ta hanyar maslaha.

Daga nan ya bukaci al’ummar jiharnan musamman magoya bayan jam’iyyar APC da su bayar da cikakken hadin kai da goyan baya domin samun nasarar gudanar da ayyukan kwamatin.

A nasa shugaban jam’iyyar APC na jiha, Aminu Sani Gumel, ya yiwa kwamatin lale marhabun zuwa jihar Jigawa, tare da bada tabbacin hadin kai da goyan bayan al’ummar jihar nan musamman magoya bayan jam’iyyar APC domin cimma burin da aka sanya a gaba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: