Jam’iyyar APC ta yi Allah-wadai da zanga-zangar da magoya bayan jam’iyya NNPP ke yi a jihar Kano

0 196

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta yi Allah-wadai da zanga-zangar da magoya bayan jam’iyya mai mulki a jihar NNPP ke ci gaba da yi a jihar, biyo bayan sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tsige Gwamna Abba Yusuf.

Jam’iyyar adawa ta APC ta ce zanga-zangar da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka yi ya saba wa yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyu a jihar suka sanya wa hannu gabanin zaben gwamna da da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

Gidan rediyon Sawaba ya ruwaito cewa tun a makon da ya gabata ne ake ta zanga-zanga a Kano bayan da aka gano cewa akwai sabani a hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na korar Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano. Da yake zantawa da manema labarai jiya a Kano, jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon Kwamishinan Raya Karkara, na jihar Alhaji Musa Kwankwaso, ya yi zargin cewa gwamnatin Abba Kabir  Yusuf  ke daukar nauyin bayar da kudada ga masu zanga-zangar domin tada zaunar tsaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: