Jam’iyyar NNPP Ta Yi Watsi da Jita-Jitar Murabus Din Mataimakin Gwamnan Jihar Kano

0 131

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi Allah-wadai da kalaman Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, wanda ya bukaci Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya yi murabus.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Ibrahim Karaye, ya fitar, jam’iyyar ta ce kundin tsarin mulki har yanzu ya ba Mataimakin Gwamnan damar ci gaba da rike mukaminsa.

Jam’iyyar ta bayyana cewa kalaman kwamishinan sun biyo bayan matakin da Gwarzo ya dauka na kin sauya sheka tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu daga cikin mataimakansa zuwa jam’iyyar APC.

A cewar NNPP, Gwarzo na da hakkin ci gaba da gudanar da aikinsa kasancewar shi da gwamnan an zabe su ne a karkashin tuta daya.

NNPP ta bukaci bangaren zartarwa na jihar da ya guji tsoma baki na siyasa, tare da mai da hankali kan ayyukan da kundin tsarin mulki ya dora musu.

“Yana da muhimmanci Mataimakin Gwamna ya ci gaba da rike mukaminsa domin ingantacciyar shugabanci a jihar,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta kuma lura cewa Kwamishinan Yada Labarai ba ya cikin fafutukar da ta kai ga kafa wannan gwamnati, tare da ba shi shawarar ya yi shiru.

Leave a Reply