NNPCL da Wasu Gidajen Mai A Najeriya Sun Kara Farashin Man Fetur Sau Biyu Cikin Awanni 24

0 148

Kamfanin Man Fetur na Kasa na Najeriya, Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL), tare da wasu gidajen mai sun kara farashin man fetur sau biyu cikin awanni 24.

Wakilin SAWABA da ya duba wasu gidajen sayar da man NNPCL a ranar Alhamis ya gano cewa an daidaita farashin litar man fetur zuwa N875, daga N839 da aka kara a ranar Laraba.

An fara aiwatar da sabon farashin a gidajen man NNPCL da ke Gwarimpa, Kubwa Express, Wuse Zones 6 da 4, da sauran sassan Babban Birnin Tarayya.

Wata ma’aikaciyar gidan mai da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa SAWABA cewa sabon farashin ya fara aiki ne a ranar Alhamis.

“An sanar da mu tun jiya da daddare (Laraba), amma mun fara sayarwa a kan N875 kowace lita a ranar Alhamis. A baya muna sayarwa a kan N839 kowace lita, daga N815,” in ji ta.

Wannan na nufin cewa cikin awanni 24 kacal, kamfanin mallakin gwamnati ya kara farashin man fetur da N60 a kowace lita.

NNPCL ba shi kadai ne ya kara farashin man fetur ba, domin Ranoil, Empire Energy, da sauran gidajen mai a Babban Birnin Tarayya sun kara farashinsu zuwa tsakanin N899 da N900 kowace lita.

A halin yanzu, gidajen man MRS sun kara farashin man fetur da N100 zuwa N839 kowace lita.

Daya daga cikin manajojin gidan man MRS a Abuja ya tabbatar wa SAWABA a ranar Alhamis cewa har yanzu farashin su na nan a kan N839.

Wannan ci gaban na zuwa ne kwanaki kadan bayan matatar Dangote da masu rumbunan ajiya suka kara farashin man daga matakin “ex-depot” zuwa sama da N799 kowace lita.

Wannan mataki ya haifar da karin farashin man fetur sosai a fadin kasar.

Leave a Reply