Jihar jigawa a yan kwanakin nan ta zama wani maudu’in tattaunawa ta mummunar siga

0 255

Hakan ya biyo bayan hukuncin Babbar kotun jihar na aike da wasu matasa zuwa gidan gyaran hali har karshen rayuwa su, sakamakon samun su da aikata laifuka masu alaka da aikata luwadi ga kananan yara.

A cikin makwanni biyu da suka gabata, an yanke wa wasu mutane uku hukuncin bayan sun aikata laifin a kan yara kusan 10.

Kotu ta samu mutane daban-daban masu shekaru tsakanin 27 zuwa sama da aikata laifin ga yara a kananan hukumomi daban-daban, hakan dai ya tayar da hankalin iyaye da malaman addinin Musulunci da sauran masu ruwa da tsaki.

A wata tattaunawa da jaridar daily trust ta yi da wani malamin Jami’ar Tarayya dake  Dutse, Sarki Suleiman, ya bayyana lamarin a matsayin ta’addancin da ya saba wa dabi’ar dan Adam.

A cewar Suleiman, ya bayyana cin zarafin yara maza da iyaye mata a matsayin wani dalili da ke sanya yaran su fada mummunar ta’adar.

Haka kuma daya daga cikin iyaye kuma mazaunin Dutse, Auwalu Adamu, ya ce daya daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalar shi ne talauci. A nasa bangaren, wani malami, Rabiu Aliyu Garin Gabas, ya ce galibin iyaye maza suna barin komai, ciki har da tarbiyyar yara ga iyaye mata; kuma al’amura suna tafiya ba daidai ba ne yayin da mutane suka bar nauyin da ke kansu ga wasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: