Jihar Jigawa Na Kara Matsa Kaimi Wajen Kulle Iyakarta

0 96

Kwamatin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa yaja hankalin jami’an tsaro dake kula da kan iyakar jihar Jigawa da Yobe a garin Birniwa da su rubanya kokari wajen tabbatar da ganin cewa matafiya daga jihohin Borno da Yobe ba su hauro zuwa Jigawa ba, domin dakile yaduwar cutar corona.

Shugaban kwamatin, Alhaji Aliyu Ahmad Aliyu, ya bayyana bukatar hakan lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin zuwa ziyara kan iyakar a garin Birniwa.

Shugaban wanda ya mika kyallayen rufe fuska da hanci da sinadaran wanke hannu ga jami’an tsaro dake kula da kan iyakar, yace sun ziyarci yankin ne domin tabbatar da cewa jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya na gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata.

Aliyu Ahmad Aliyu ya yabawa baturen ‘yan sanda na yankin, Mustapha Muhammad Lawan bisa sadaukar da kai a aikinsa.

Daga nan sai yayi kira ga shugaban karamar hukumar Birniwa, Alhaji Muhammad Jaji Dole ya samar da kayan aikin da ake bukata ga jami’an tsaron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: