Ma’aikatan Jihar Jigawa Zasu sake zaman Gida na Mako Biyu

0 100

Gwamnatin jihar Jigawa ta umarci dukkanin ma’aikatanta da su cigaba da yin aiki daga gida na tsawon makonni 2, yayin da ta tsame ma’aikatan sashin ayyuka na musamman, da suka hadar da na ma’aikatar lafiya, kudi da albarkatun ruwa.

Shugaban kwamatin yaki da cutar na jihar kuma kwamishinan lafiya Dtr. Abba Zakar, shine ya sanar da hakan ga manema labarai a jiya talata a birnin Dutse.

Tun dai a ranar 24 ga watan Maris da ya gabata ne gwamnatin Jigawa, ta umarci ma’aikatan da suyi aiki daga gida na tsawon makonni 2, a kokarin daukar matakan dakile yaduwar cutar Corona.

To sai dai a ranar 7 ga watan Aprilu, gwamnatin ta tsawaita umarnin na wasu kwanakin 14, da a jiyane ne 21 ga watan da muke ciki, wa’adin ya cika.

Shugaban kwamatin yace a karshen wa’adin umarnin, gwamnati zata nazarci lamarin, inda zata duba yuwuwar dage dokar ko sake tsawaitata.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka samu rahoton billar cutar Corona a karamar hukumar Kazauren jihar Jigawan, abin da ya sanya gwamna Badaru, ya kakaba dikar zaman gida a yankin, domin dakile bazuwar cutar, bayan mika mara lafiyar cibiyar killace masu cutar dake birnin Dutse.

Leave a Reply

%d bloggers like this: