Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya NiMet ta yi gargadi game da matsanancin zafi da zai shafi jihohi 18 na Arewacin Najeriya ciki har da Gombe, da Kano, da Katsina, da Zamfara da kuma Babban Birnin Tarayya, inda ake hasashen zafin zai kai har zuwa digiri 40 na Celsius daga yau Asabar.
A cikin sanarwar da aka fitar, hukumar ta ce bayan ruwan sama na kwana uku da ya gabata, iska mai danshi da sararin sama marar gajimare zai haddasa karin zafi da rashin jin dadi a jikin mutane.
Shugaban sashen yanayi na Gombe, Gayus Musa, ya shawarci jama’a su guji fitowa rana sosai, sannan su sha ruwa da yawa, su kuma zauna a wurare masu iska da sanyi don kare kansu daga matsalolin lafiya.
Ya kara da kiran iyaye da su kula da yara da tsofaffi, tare da rokon hukumomi da su fadakar da jama’a game da hadarin zafin rana da hanyoyin da za a kare kai.