Jihohin Oyo da Osun da Ogun sune suka fi yawan wadanda suka nemi rubuta jarabawar JAMB ta wannan shekarar

0 92

Bayanai da hukumar samar da guraben karatu a makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta wallafa ya nuna cewa jihohin Oyo, Osun da Ogun ne suka fi yawan wadanda suka nemi rubuta jarabawar JAMB ta bana.

Jihoshin ukun kuma sun sami jumillar wadanda suka nemi rubuta jarabawar fiye da jumillar jihohi 10 da ke da mafi karancin wadanda suka nemi rubuta jarabawar.

Jumillar wadanda suka nemi rubuta jarabawar daga jihoshin uku sun kai dubu 227 da 706 daga cikin dalibai miliyan 1 da dubu 351 da 215 na kasarnan da suka zauna jarabawar shiga manyan makarantu ta bana, daya daga cikin abubuwan da ake bukata ga kowane dalibi a kasarnan da ke neman gurbin karatu a makarantun gaba da sakandire.

Kazalika, a jerin jihoshin dake da mafi karancin wadanda suka nemi rubuta jarabawar akwai ta karshe jihar Zamfara mai dalibai dubu 6 da 545; sai Babban Birnin Tarayya mai dalibnai dubu 7 da 20; sai Sokoto mai dalibai dubu 10 da 302; sai Yobe mai dalibai dubu 11 da 946; sai Jigawa mai dalibai dubu 13 da 784.

Leave a Reply

%d bloggers like this: