Jirgin kasa yayi hatsari a hanyar Abuja zuwa Kaduna

0 307

Wani jirgin ƙasa da ke dauke da fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna ya kauce hanya a safiyar Talata, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin tashin hankali da rudani.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan jirgin ya bar Abuja da misalin ƙarfe 11 na safe, inda mutane suka fara neman tsira da rayuwankan su.

Ba a tabbatar da adadin raunuka ko mace-mace ba, sannan har yanzu Hukumar Jiragen ƙasa da Ƙasa (NRC) ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Rahotanni daga jami’an tsaro sun ce an tura sojoji zuwa wurin don tallafa wa fasinjojin da abin ya shafa.

Har yanzu ana ci gaba da tattara bayani game da abinda ya janyo aukuwar lamarin,

Leave a Reply