Yau ranar Hausa ta Duniya,Tunawa da Gudunmawar Harshen Hausa a Fadin Duniya

0 360

A Kowacce 26 ga watan Agusta, rana ce da aka ware don gudanar da bikin ranar Hausa, wanda ke gudana tsakanin miliyoyin al’ummar Hausawa da ke sassa daban-daban na duniya, kodayake bikin yafi kankama tsakanin al’ummomin yankin yammacin Afrika yankin da ke da yawan wannan ƙabila.

A shekarar 2015 aka faro bikin wannan rana, don nuni da kuma duba irin gagarumar gudunmawar da harshen na Hausa mafi yawan jama’a a yammacin saharar Afrika ke bayarwa.

Bayanai sun yi nuni da cewa ƙarƙashin jagorancin wani ɗan Jaridar Abdulbaki Aliyu Jari ne aka samar da wannan rana tare da fara bikinta, cike da fatan ɗaga darajar wannan harshe da ke ci gaba da bunƙasa zuwa sassa daban-daban na duniya.

Ana kuma jan hankalin jama’a kan yi amfani da harshen Hausa a rubuce-rubuce, a tattaunawa da mu’amala, musamman a shafukan sada zumunta.

Wannan ya sa ake ganin Ranar Hausa ta Duniya a matsayin wata hanya ta kare harshen da kuma ƙarfafa amfani da shi a fannoni na zamani kamar kimiyya, fasaha da kasuwanci.

Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa.Kawo yanzu dai babu sahihin bayani kan asali ko kuma lokacin da aka fara amfani da harshen Hausa a ban ƙasa, amma batutuwa da dama na alakanta saurin yaɗuwarsa da fataucin da aka san Bahaushe.

Hassana sulaiman ta hada mana rht kan ranar hausa…

Leave a Reply