A karon farko, kamfanin Twitter, ya ce zai dauki ma’aikata a nahiyar Afirka inda ya shirya bude cibiyarsa a Ghana nan gaba kadan. Kamfanin ya ce zai dauki ma’aikata.

Kamfanin na Twitter, ya bi sahun takwaransa a bangaren sada zumunta na zamani Facebook da ma karin wasu 11 wajen shiga kasashe nahiyar ta Afirka.

A wata ziyarar da ya kai kasashen Najeriya da Ghana da Ethiopia da ma Afirka ta Kudu a bara, shugaban Twitter, Jack Dorsey, ya ce Afirkar za ta kasance a kan gaba wajen tsara makomar ci gaban wannan duniya.

Tuni ma dai aka tallata wasu manyan mukamai 11 da za a dauki ma’aikata a Ghana, a fannonin da suka hada da kwarraun injiniyoyi da na kasuwanci da ma wadanda suka kware a harkar sadarwa.

Asalin labarin;

https://www.dw.com/ha/twitter-zai-kafa-reshe-a-afirka/a-57175013

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: