Kungiyar Barcelona ta fi ko wacce kungiya kudi a duniya

0 120

Barcelona ta doke Real Madrid a matakin kungiyar kwallon kafa da take kan gaba a arziki a fadin duniya.

Mujallar kididdigar kudi ta Forbes ce ta bayyana hakan ranar Litinin, inda ta ce kungiyar ta Camp Nou tana da dalar Amurka biliyan 4.76.

Real Madrid wadda ta rike mataki na daya karo biyar a baya ta koma ta biyu mai dalar Amurka biliyan 4.75.

Forbes ta ce matsakaicin kudin shiga da kungiyoyi 20 suka samu a kaka biyu ya karu zuwa kaso 30 cikin 100 wato dalar Amurka biliyan 2.28.

Kungiyoyin sun samu wannan arikin duk da kalubalen da cutar korona ta haddasa da ta kai ba sa samun kudin shiga kallon wasa ido da ido a kowanne mako.

Rashin shiga stadiya sakamakon tsoron yada cutar korona ya sa kungiyoyin sun yi hasarar dalar Amurka miliyan 441 a kakar bara wato kaso 9.6 cikin dari tun daga 2017/18.

Leave a Reply

%d bloggers like this: