Manyan kasashen duniya za su gudanar da taron kwanaki biyu a yunkurin rage yawan tiririn da ake fitarwa da ke dumama yanayi.

A babban taron koli kan yanayi da ke tafe, ana sa ran Shugaban Amirka, Joe Biden zai amince da rage yawan hayakin da kasar ke fitarwa, a kokarin da manyan kasashen duniya ke yi na ceto duniya daga barazanar Sauyin yanayi. Taron na kwanaki biyu da za a gudanar ta bidiyo saboda annobar corona, zai sami halartar shugabanin kasashen akalla arba’in. Biden zai yi kokarin nusantar da sauran takwarorinsa kan illolin fitar da yawan iskar gas mai dumama yanayi ga tattalin arziki da lafiyar al’ummar duniya.

Amirka a yayin gwamnatin Barack Obama ta yi alkwarain rage tiririn da ke dumamma yanayi da ta ke fitarwa da kashi ashirin da takwas amma gwamnatin Biden ta shirya ninka shi zuwa kashi hamsin zuwa hamsin da biyu nan da shekarar 2030. Masana dai na cewa amfani da bakin gawayi wurin samar da lantarkin da China ke yi, shi ne mafi hadari ga muhalli a cikin hanyoyin da ake samar da lantarki a duniya. 

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: