Bayan sace daliban jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya, ‘Yan bindigar sun kara afkawa a ranar Alhamis zuwa wani asibiti tare da sace wasu ma’aikatan lafiya a babban aisibitin jihar da ke karamar hukumar Kajuru.

Shugaban karamar hukumar Kajuru, Cafra Casino, ya yi kira ga mutanen su kwantar da hankali tuni an fara gudanar da bincike kan ma’aikatan lafiya biyu da aka sace.

Rahotanni daga Kaduna na cewa har yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba kan lamarin, Wani babban likita a asibitin ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar na dauke da manyan makamai ne masu hadari lokacin da suka shiga harabar asibitin ta katanga.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar da suka kutsa asibitin sun sace wasu ma’aikatan jinya biyu da ke aikin dare wadanda suka ce su likitoci ne.

Asalin Labarin: https://www.bbc.com/hausa/live/labarai-56842862

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: