Kasar Amurka da kawayenta na ci gaba da debe mutane daga kasar Afghanistan

0 503

Kasar Amurka da kawayenta na ci gaba da debe mutane daga kasar Afghanistan, adaidai lokacin Shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ke son kwashe dubun nan mutane kafin karewar wa’adin 31 ga watan Agusta da suke son janye sojojinsu daga kasar.

Sama da mutane dubu 70 ne yan asalin kasar Afghanistan da bakin dake zaune a kasar aka kwashe daga filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul.

Tindaga ranar 14 ga wannan watan, kafin yan Taliban su isa babban birnin kasar.

Awani labarin kuma bankin duniya ya dakatar da miliyoyin kudaden tallafi da yake turawa kasar Afghanistan, wanda yafara bata wannan tallafin tindaga 2002 da dala biliyan 5 da miliyan 3, wadanda aka gudanar manyan ayyuka 27 a fadin kasar.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan asusun bada lamani na duniya IMF ya dakatar da tura kudaden tallafi ga kasar.

Hukumonin agaji na duniya na ikirarin cewa za’asamu bullar cututtuka a Afghanistan, kamar yanda babban darakta a hukumar abinci ta majalissar dinkin duniya David Beasley ya fadawa manema labarai.

Inda yace akalla mutane miliyan 14 ne, wato kaso 1 ciki na mutanen Afghanistan zasu fuskanci karancin abinci

Leave a Reply

%d bloggers like this: