Kasar Amurka ta aika tallafin abinci zuwa Maiduguri

0 106

Kasar Amurka ta aika tallafin abinci zuwa ga waɗanda ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wata sanawarwa da hukumar raya ƙasashe ta gwamnatin Amurkar wato USAID ta fitar, ta ce za ayi amfani da ƙungiyoyin agaji na MDD da kuma waɗanda take hulɗa da su wajen bayar da tallafin.

“Abin damuwa ne matuka ganin yadda ambaliya ta ɗaiɗaita al’ummomi a Maiduguri da wasu sassan jihar Borno, abin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi. Muna miƙa sakon ta’aziyya zuwa ga iyalan da abin ya shafa,” in ji Amurka.

USAID ɗin ta ce za ta yi aiki da shirin samar da abinci na duniya (WFP) wajen kai tallafin abincin zuwa sansanoni huɗu da aka tsugunar da waɗanda ambaliyar ta ɗaiɗaita, kuma an samu kai ga mutane sama da 67,000 a cikin kwanaki da suka gabata.

Shi ma WFP ya ce yana taimakawa mata masu ciki da kuma yara ƴan ƙasa da shekara biyar wajen samun abinci mai gina jiki.

Haka kuma, Amurkar ta ce tana taimakawa wajen kai abinci wuraren da ke da wahalar kai wa a Maiduguri da kuma faɗin jihar Borno ta hanyar amfani da jiragen sama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: