Kasar China ta sanar da cewa kimanin mutane fiye da dubu 20 ne suka harbu da cutar Corona a wannan satin

0 17

Kasar China ta sanar da cewa kimanin mutane dubu 13 da 146 ne suka harbu da cutar Corona a ranar Asabar.

Wannan shine adadi mafi yawa na mutanen da suka harbu da cutar Corona tun bayan bullar cutar shekaru 2 da suka gabata.

A birnin Shanghai kimanin mutane Miliyan 25 ne aka bukaci su zauna a gida domin hana yaduwar cutar.

An rawaito cewa birnin a yanzu hakan birnin shine cibiyar yaduwar cutar a kasar ta China baki daya.

Manema Labarai sun rawaito cewa kimanin mutane 438 ne suka harbu da cutar a jiya, baya ga wasu mutane dubu 7 da 788 da suka nuna alamun kamuwa da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: