Tsohon Gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje zai fice daga jam’iyar APC zuwa PDP a gobe Laraba

0 60

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Sanata Danjuma Goje, zai fice daga Jam’iyar APC zuwa PDP a ranar Laraba.

Sanata Goje wanda a yanzu haka shine Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa, zai kowa Jam’iyar PDP tare da dubban magoya bayansa, biyo bayan yadda suka samu baraka tsakanin sa da Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar mai ci.

Wani kusa a Jam’iyar PDP shine ya bayyana hakan ga manema labarai, bayan ya bukaci a sakaya sunan sa, inda ya ce Sanata Goje zai koma PDP tare da Miliyoyin magoya bayan sa a sakatariyar Jam’iyar PDP ranar Laraba.

Majiya ta ce duk da cewa Sanata Goje da Hassan Dankwambo basa tare tsawon lokaci saboda bam-bamce-bam-bamcen Siyasa, amma sun amince suyi aiki tare domin ciyar Gombe gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: