Kasar Saudiyya ta kara yawan kamfanonin jirge da za su yi jigilar maniyyata a aikin Hajjin 2024

0 191

Kasar Saudiyya ta kara yawan kamfanonin jirgin yawo da za su yi jigilar maniyyatan a aikin Hajjin 2024 zuwa 40 daga 10 a kasar nan.

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce sassaucin da Saudiyya ta yi zai kara saukakawa Najeriya wajan jigilar maniyyatan kasar.

Da farko NAHCOn ta tantance kamfanonin jirgin yawo 110 domin jigilar maniyyatan kasar nan a 2024.

Sai dai Ma’aikatar Aikin Hajji ta Saudiyya ta kayyade kashi 5% na kamfanonin jirgin yawo na kasashe masu alhazai damar jigilar.

Da haka ne Najeriya ta kare da samun kamfanoni 10, kafin Saudiyyar ta sassauta gabanin aikin Hajjin 2024 da ke tafe.

Sanarwar NAHCON ta ce kamfanonin jirgin yawo 40 da suka fi samun maki daga cikin 110 da ta tantance ne za su yi aikin a bana. Ta kara da ragowar 70 din da da su hada kai da 40 din da aka zaba wajen gudanar da aikin cikin nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: