Yan majalissa 109 sun sadaukar da albashinsu ga iyalan wadanda harin Bam ya rutsa da su a Tudun Biri
Yan majalissa 109 na kasar nan sun sadaukar da albashinsu na wata daya, wanda ya kai Naira Miliyan N109 ga iyalan wadanda harin Bam ya rutsa da su a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya bayyana hakan a gidan gwamnatin Kaduna a lokacin da ya jagoranci wata babbar tawaga ta majalisar zuwa jihar a jiya Lahadi.
Sanatocin sun samu tarba daga gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.
Sanata Barau, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya ce za a mika gudunmawar ne zuwa asusun gwamnatin jihar domin mika wa wadanda lamarin ya rutsa. Gwamna Uba Sani ya mika godiyarsa ga Sanatocin da suka bayar da wannan gudunmawar.