Hatsarin tirela ya yi ajalin mutane 16 yayin da wasu 27 suka jikkata a Jihar Kaduna

0 128

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a jihar, Kabir Nadabo ya ce hatsarin ya auke ne jiya Lahadi.

Nadabo ya ce wata tirela kirar DAF dauke da mutane 65 ce ta kwace ta fada a cikin wani rami da asuba.

Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kusa da kauyen Audu Jangwam a kan Babbar Hanyar Kaduna-Abuja.

Yayi zargin hatsarin ya auku ne a sakamakon gudun wuce kima da kuma gajiyar direba. Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa an kai wadanda suka jikkata asibiti

Leave a Reply

%d bloggers like this: