Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar bashin Naira tiriliyan 1.5 a ma’aikatar Ayyuka

0 223

Ministan Ayyuka, David Umahi ya ce Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar bashin Naira tiriliyan 1.5 a ma’aikatar.

Umahi ya ce ma’aikatar ta kafa kwamitoci shida saboda yankunan siyasa shida na kasar nan domin tantance basukan da ‘yan kwangila ke bin ta.

Ya ce, kwamitocin za su tantance takardun shaidar bashin da gwamnati ta ba wa ’ya kwangilar da Buhari ya sauka daga mulki.

Za kuma su tantance takardun shaidar bashin da suke bin ma’aikatar daga hawan Shugaba Tinubu zuwa yanzu.

Umahi ya ce tantance basukan da kuma sauyin farashi da aka samu na da muhimmanci, lura da hauhawan farashin kaya.

Don haka ya shawarci ’yan kwangilar da su zo gaban kwamitin domin tantancewa a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja. Sakataren yada labaran ma’aiaktar, Orji Uchenna Orji ya ce, za ya yi tantancewar ne daga ranar Talata 12 zuwa Juma’a 22 ga watan  Disambar da muke ciki daga karfe 9 na safe zuwa 7 na dare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: