Mata zasu samu ilimi tare da sana’a a karkashin sabuwar gwamnatin jihar Katsina

0 156

Mai ba Gwamnan Jihar Katsina shawara ta musamman kan ilimin ‘ya’ya mata a jihar, Hajiya Jamila Abdu Mani, ta bayyana cewa duk wata ‘ya mace a jihar za ta samu ilimi tare da sana’a a karkashin wannan sabuwar gwamnatin.

Ta yi wannan alkawari ne a wajen mika kudi naira N10,000 ga wasu ‘yan matan da aka horar da su kwanan nan da suka kammala karatu a cibiyar koyar da sana’o’i a jihar, inda ta kara da cewa, koyarwa da sana’o’i, ilimin addini da na zamani shi ne abu mafi muhimmanci da gwamnatin jihar ta sa a gaba.

Hajiya Mani ta kara da cewa, tuni gwamnati ta aike da kudirin dokar hana tallace-tallace a lokacin makaranta zuwa majalisar dokokin jihar domin samun amincewarta na zartar da kudirin dokar, domin bunkasa makarantun jihar. A yayin da ta jaddada cewa, gwamnati mai ci za ta samar da hanyoyin da za a kawo karshen duk wani kalubalen da ke addabar ‘ya’ya mata a jihar, ta ce an kafa cibiyar tuntuba da cin zarafin mata a kwanan nan domin magance matsalar cin zarafin mata a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: