Kimanin Sojojin Najeriya 62 ne aka tura zuwa ƙasar Mali domin yin atisayen dawo da zaman Lafiya a ƙasar

0 213

Kimanin Sojojin Najeriya 62 ne aka tura zuwa Kasar Mali domin yin atisayen dawo da zaman Lafiya a Kasar.

Mataimakin Mai Bada Horo na Rundunar Sojin Najeriya Brigadier Generla Hassan Dada, shine ya bayyana hakan a jiya, a lokacin da ake bikin yaye Sojojin bayan sun samu horo kan ayyukan dawo da zaman Lafiya, wanda aka gudanar a barikin Jaji dake Jihar Kaduna.

An gudanar bikin ne a daidai lokacin da suke shirye-shiryen tafiya birnin Bamako na kasar Mali, kuma zasu bar Najeriya ne cikin gaggawa bayan an rantsar dasu.

General Dada, ya bayyana cewa rundunar Sojin Najeriya bazata lamunci kowanne irin rashin da’a ba, daga wurin Dakarun a lokacin da suke gudanar da ayyukan su a kasar.

Kazalika, ya shawarce su su kasance masu bin dokoki da ka’idojin aikin Soja a lokacin da suke gudanar da ayyukan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: