Kimanin yara miliyan 14 da dubu 700 ‘yan Najeriya ne zasu fuskanci yunwa a wannan shekarar – UNICEF

0 81

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa kimanin yara miliyan 14 da dubu 700 ‘yan Najeriya, ‘yan kasa da shekaru biyar ne za su fuskanci matsananciyar rashin abinci mai gina jiki idan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki ba su dauki matakin gaggawa ba.

Shugaban sashin kula da abinci na UNICEF a Najeriya Nemat Hajeebhoy ce ta bayyana hakan jiya a Abuja a wani taron manema labarai da majalisar kula da ingancin abinci ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki suka shirya.

Jami’ar ta UNICEF, wacce ta ce Najeriya na cikin wani yanayi na gaggawa na abinci mai gina jiki saboda ta yi asarar kashi 15 cikin 100 na ma’aunin tattalin arzikinta, na GDP, sakamakon yawaitar rashin abinci mai gina jiki a kasar.

Ta ce mummunar ambaliyar ruwa, asarar gonakin noma, hauhawar farashin kayayyaki, da matsalar tsaro a wasu sassan da sauran abubuwan da ke shafar samar da abinci mai gina jiki a kasar, wanda a cewarta, zai iya kara tabarbarewa a shekarar 2023, inda yara za su fi fama da matsalar.

Nemat Hajeebhoy ta kara da cewa farashin kayan abinci ya tashi da kashi 23 cikin dari a cikin shekara guda da ta wuce, wanda hakan ya sa magidanta ke shan wahala wajen samar da abinci mai gina jiki ga iyalansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: