Shugaba Buhari ya amince da sakin ton dubu 12 na hatsi a matsayin kayan agaji ga wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa

0 86

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da sakin ton dubu 12 na hatsi a matsayin kayan agaji ga wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a fadin kasar nan.

Ministar harkokin jin kai da kula da annoba da walwalar jama’a, Hajiya Sadiya Umar-Farooq, ce ta bayyana haka a wajen taron tattaunawa na mako-mako da kungiyar sadarwar shugaban kasa ta shirya, jiya a Abuja.

A cewar ministar, ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta isar da kayan tallafin ga Jihohi 28 na tarayyar kasar nan.

Ministar ta sanar da cewa, kwamitin shugaban kasa kan bada agaji da farfado da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a karkashin jagorancin hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, ya samar da kayan abinci iri-iri na sama da naira miliyan dubu 1 da miliyan 500 a matsayin tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kasar nan.

Ta bayyana cewa, a wani bangare na matakan dakile karkatar da kayayyakin agajin, ko kuma boye kayayyakin agajin, a cewar ta an shigar da dukkan masu ruwa da tsaki da jami’an tsaro wajen rabon kayayyakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: