An tsare wasu yan TikTok biyu saboda bata sunan gwamnan jihar Kano

0 85

Wasu ’yan TikTok guda biyu, Mubarak Muhammad da aka fi sani da Uniquepikin da Nazifi Muhammad, an tsare su a gidan yari bisa zargin su da bata sunan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a wani wasan barkwancin da suka yi.

An rawaito cewa mutanen biyu sun hada bidiyon da suka nuna gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin dan siyasa mai cin hanci da rashawa, wanda ya siyar da duk wani filin gwamnati a jihar.

‘Yan sanda sun gurfanar da su a gaban Kotun Majistare mai lamba 58, dake No-man’s-land, karkashin jagorancin Alkalin Kotun, Aminu Gabari.

Lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen, ‘yan TikTok din biyu sun amsa laifin da ake tuhumar su na hada baki da kuma bata sunan gwamnan.

A saboda haka alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: