Kotu Ta Bayar Da Belin Matar Da Ta Cakawa Mijinta Wuka A Kano

0 205

Babbar kotun jihar Kano mai lamba daya ta bayar da belin Fatima Hamza da aka fi sani da Hanan,wacce ake zargi da yunkurin kashe mijin ta Said Hussein bayan da ta caka masa wuka.

Jagorar kungiyar Mata lauyoyi ta kasa FIDA Barrister ta shaidawa kotun cewar tuhumar da yansanda suka yiwa Hanan bata da tushe domin fada suka yi ya bangashe mata hakora ita kuma ta soka masa wuka,suka yi kare jini biri jini.

Bar Lamido Abba soron dinki dake zaman lauyan gwamnati bai yi suka ba, Don haka kotu ta bayar da Hanan beli nan take.

Labarin bayar belin wannan mata dai ya fito daga shafin Facebook din wani gogaggen dan Jarida a Kano Nasir Salis Zango a safiyar Yau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: