‘ku cigaba da sanya takunkumin kariya domin Korona na kara yaduwa,’ -WHO

0 88

Ya yin da ake nuna damuwa kan yadda cutar korona ke kara yaduwa a kasar China, da wasu sassan duniya, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu amfani da takunkumin rufe fuska ya na bada kariya daga kamuwa da korona tare da bukatar a ci gaba da amfani da shi.

A sabbin alkalumman da WHO ta fitar, ya nuna korona na kara yaduwa a wasu kasashe musamman a wannan lokacin da ake fama da tsananin sanyi a wasu kasashen duniya.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Hukumar Lafiya na aiki kafada da kafada da gwamnatoci da kungiyoyi kan matakin dauka a wannan gabar da ake murnar bako ya tafi, ashe ya na labe a bayan gari.

A baya-bayan nan cutar korona ta kara tasowa gadan-gadan a kasar China, wanda akai amanna nan ne tushen koronar. Hukumomi sun sanar da mutuwar mutane da dama da wanda ke asibiti.

-BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: