Gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele ya koma bakin aiki bayan hutun da yake yi a kasar waje

0 150

Gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele ya koma bakin aiki bayan hutun da yake yi a kasar waje.

Gidan Rediyon Sawaba ya bayar da labarin yadda jami’an tsaron SSS suka mamaye hedikwatar CBN tare da kwace ofishin Godwin Emefiele a jiya da yamma.

Duk da cewa kakakin hukumar SSS, Peter Afunanya, ya musanta mamayar, inda ya bayyana rahoton a matsayin labaran karya, wasu majiyoyi masu inganci a CBN sun tabbatar da rahoton mamayar, tare da wallafa hotuna.

Godwin Emefiele, wanda ya tafi hutu a watan Disambar 2022, ya koma bakin aiki a jiya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ya fitar, ta ce gwamnan ya koma aiki da sabon kuzarin gudanar da aikinsa gabanin taron kwamitin kula da harkokin kudi na farko na shekarar wanda aka shirya gudanarwa a ranar 23 zuwa 24 ga watan Janairun da muke ciki.

Yayin da yake gode wa jama’a bisa yadda suka yi imani da bankin, babban bankin ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da ba wa manufofin bankin goyon baya da nufin tabbatar da ingantaccen tsarin hada-hadar kudi da tattalin arzikin kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: