Gwamnatin jihar Jigawa ta tura kudaden yarjejeniyar karatu na daliban Informatics Kazaure zuwa kasar Singapore

0 156

Gwamnatin jihar Jigawa ta tura kudaden yarjejeniyar karatu na daliban makarantar koyar da fasahar sadarwa ta zamani dake Kazaure zuwa kasar Singapore.

Shugaban makarantar, Farfesa Babawuro Usman ya sanar da hakan a lokacin da yake tilawar nasarorin da makarantar ta samu a shekarar 2022.

Yace an biya kudaden makarantar ne ga daliban dake karatun kwasa kwasan dake da nasaba da kasashen waje.

Farfesa Babawuro Usman ya kara da cewa sau uku ake biyan kudaden makarantar ga kasar Singapore, inda yace a diban daliban farko a shekarar 2022 sun biya dala dubu 45 sai diban daliban na biyu da suka tura kudi dala dubu 45.

Shugaban makarantar yace gwamnati ta biya wasu kudaden a matsayin kudaden yarjejeniya na shekara-shekara.

Yace suna karbar kudaden makaranta ga daliban da ba ‘yan Jigawa bane inda suka tara dala dubu 15 a zangon farko sai zango na biyu dala dubu 13 a zango na uku dala dubu 12.

Leave a Reply

%d bloggers like this: