Ku Tuba Daga Amfani Da Tsohuwar Hanyar Noma, Ku Rungumi Ta Zamani – Pantami

0 184

Daraktan hukumar bunkasa harkokin sadarwa ta kasa Dr. Isa Ali Pantami, ya bukaci ‘yan Najeriya da su riki noman zamani ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa.

Pantami ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in gudanarwa na ofishinsa Dr. Aminu Magaji, yayin wani taron harkokin samar da ayyukan yi ga al’umma.

Taron da aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria jihar Kaduna, ya tabo batutuwan da suka shafi matsalolin da ake fuskanta a bangaren noma.

Ya ce hanyar cigaban noma a wannan zamani ita ce amfani da hanyoyin sadarwa domin cigaban tattalin arzikin kasa.

Kazalika Pantami ya ce hanyar inganta noma ita ce samar da iri da kuma takin zamani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: