Nigeri Da Holland Zasu Yi Hadaka Don Cigaba – Osinbajo

0 186

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buahari ta nuna sha’awarta wajen hadin gwiwa da kasar Netherland domin bunkasa cigaban al’umma.

Osinbanjo ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin Najeriya Abuja, yayin da ya karbi tawagar yan kwamittin kasar wanda ministan harkokin wajen kasar Mista Sigrid Kaag ya jagoranta.

Yemi Osinbanjo ya ce gwamnatin Najeriya tana bullo da hanyoyin samar da ayyukan yi ga matasa da nufin inganta tattalin arzikin kasa.

Babban sakataren ma’aikatar masana’antu da harkokin kasuwanci Mista Sunday Akpan, ya sanya hannu kan yarjejeniyar a yayin da ya ziyarci kasar a madadin gwamnatin Najeriya.

Kazalika ya ce manufar samar da wannan harkokin kasuwanci shi ne cigaban tattalin arzikin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: