Yan Shi’a Sun Ga Ta Kansu Amma Sun Mayar Da Zazzafan Martani – Bidiyo

0 92

Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta damke mambobin kungiyar  mazhabar Shi’a su 40.

Kakakin rundunar DSP Anjuguri Manzah ya ce sun dakile wani yunkurin su na shiga cikin zauren majalisar dattawa ta kasa dake Abuja.

Ya ce mabiya mazhabar ta Shi’a sun fara wata zanga zanga lumana ne da farko domin neman a saki jagoran kungiyar Sheik Ibrahim Zakzakky, yayin da daga bisani zanga zangar ta koma tarzoma.

Manzah ya ce yayin tarzomar an harbi jami’an yan sandan su biyu a kafa, sakamakon amfani muggan makamai da duwatsu, wanda kuma yayi sanadiyyar jikkata mutane 6.

Shi'a

Kazalika ya ce yan sandan da suka samu raunuka an kai su asibiti, yayin kuma bincike ke cigaba da gudana.

Sai dai a wani bidiyon yan yanzu haka yake zagayawa a shafin Facebook, yan kungiyar sunyi ikirarin matukar jagoransu Ibrahim El-Zakzaky ya mutu to tabbas sai sun dauki mataki dai dai da yadda ya kamata.

Danganta tayi tsami tun a shekarun baya tsakanin kungiyar da gwamnatin shugaba Buhari tun bayan da yan kungiyar suka yi kicibis da ayarin sojojin kasar nan, inda haduwar tayi munin gaske. A karshe kuma aka kame shugaban kungiyar da mai dakinsa wanda har yanzu ba’a sake su ba duk kuwa da kutu ta bayar da umarnin belin nasu.

Kalli Cikakken Bidiyon Ikirarin nasu

https://web.facebook.com/labaraii24/videos/1340218346132228/?t=0

Leave a Reply

%d bloggers like this: