Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Nadin Sabbin Ministocin Buhari

0 89

Shugaban Majalisar Datttawa, Ahmad Lawan, ya furta cewa za a aikowa da Majalisar sunayen ministocin da za a nada cikin satinnan.

An dai rantsar da Shugaba Buhari a zango na 2 ranar 29 ga watan Mayu bayan ya lashe zabe a karo na 2.

Sai dai har yanzu bai rantsar da majilasr zartarwa ba saboda rashin nada ministoci bayan wata guda da rabi.

Wannan jinkirin ya sa damuwa a zukatan yan Najeriya, wadanda ke neman bahasin jinkirin na Shugaban Kasa, dayawa kuwa na kalubalantarsa akan jinkirin watanni 6 da yayi kafin ya aika da sunayen ministoci a zangonsa na farko.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Da yake nuna damuwa makamanciyar wannan, Sanata Albert Bassey Akpan, na jam’iyyar PDP daga Akwa-Ibom ya nemi Ahmad Lawan daya saka Shugaban Kasa sauken nauyin dake wuyansa akan lokaci.

Sanata Akpan yayi amfani da doka 43 a jerin dokokin majalisar dattawa.

Da yake yanke hukunci akan dokar, Sanata Ahmad Lawan ya tabbatarwa da yan majalisar cewa, Shugaban Kasa na aiki akan sunayen ministocin kuma zai iya aiko da su kafin karshen satin da muke ciki.

Talatar data gabata ne, Shugaban Kwamitin Sadarwa na Majalisar ta Dattawa, Sanata Adedayo Adeyeye, yace Majalisar Dattawa bata da hurumin tursasa Shugaban Kasa akan ya gaggauta aiko da sunayen ministoci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: