Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira ga Musulmi su koma ga Allah a wannan watan na Ramadana.

Atiku ya yi wannan kira ne a wani sakon tuwita da ya aike yana taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar shiga watan azumin Ramadana.

Sannan ya ja hankali kan muhimmanci amfani da wannan watan wajen neman tuba da sauƙin matsalolin da suka addaabi ƙasar da ci gabanta.

Ya kuma ƙara da cewa wannan lokaci ne na waiwaye da inganta kyawawan ayyukan da yawaita taimako da sadaka musamman ga maɓukata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: