Kungiyar Kwadago ta gabatar wa gwamnatin tarayya ₦200,000 a matsayin mafi karancin albashi

0 157

Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta bayyana a ranar Talata cewa mafi karancin albashi na Naira 200,000 da ta gabatar wa gwamnatin tarayya a baya na bukatar sake duba a kansa, idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki.

Kungiyar  wacce  ta bayyana  ta bakin mataimakin shugabanta na kasa, Tommy Etim, tana mayar da martani ne a ranar Talata bayan da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin mafi karancin albashi.

Etim, a wata hira ta musamman da manema labarai jiya, ya jaddada cewa, kungiyar za ta samarda shawarwarin mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ne kan yanayin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu maimakon abin da ta gabatar tun farko.

A baya dai gwamnatin tarayya ta dora alhaki ga kwamitin ma’aikata 37 da ya gaggauta tattaunawa tare da gabatar da shawarwarin sa cikin gaggawa yayin da ta umurci ma’aikatar kudi ta tabbatar da isassun kudade.

Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa ya wakilta, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin kan mafi karancin albashi na kasa a zauren majalisar zartarwa da ke Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: