Kungiyar Kwadago ta goyi bayan ‘yar bautar ƙasar da ke fuskantar barazana saboda sukar gwamnatin Tinubu

0 511

Kungiyar Kwadago ta TUC ta goyi bayan wata ‘yar bautar ƙasa mai suna Ushie Uguamaye, wanda aka fi sani da Raye, da ta ce tana fuskantar barazana saboda suka da ta yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban TUC, Festus Osifo, ya bayyana a wani shiri na Channels TV cewa matashin ya fitar da ra’ayinsa ne saboda takaici, don haka bai kamata gwamnati ta kama ta ba.

Ya shawarci gwamnati da ta kasance mai juriya da fahimtar halin da ‘yan ƙasa ke ciki, yana mai cewa dole ne ta zama mai haƙuri da masu suka.

Raye dai ta wallafa wani bidiyo a TikTok tana bayyana yadda talauci ya ta’azzara a ƙasar nan, amma har yanzu ba a samu wata sanarwa daga NYSC kan lamarin ba.

Leave a Reply