Kungiyar yan-jaridu ta kasa reshen Jigawa ta kaddamar da kwamatin shirya taron manema labarai a Dutse
Kungiyar yan-jaridu ta kasa reshen Jihar Jigawa ta kaddamar da kwamatin shirya taron manema labarai da ta kafa a nan Dutse babban birnin Jiha.
Da yake kaddamar da kwamatin, shugaban kungiyar, Comrade Isma’ila Ibrahim Dutse ya bukaci wakilan kwamatin su bullo da tsare-tsare domin ya cimma buri.
Ya bayyana wakilan kwamatin a matsayin kwararru da suka yi fice a aikin Jarida shekaru da dama.
Ya ce an kafa kwamatin ne da nufin karfafa aikin Jarida ta hanyar isar da sakonni zuwa ga wadanda abin ya shafa a Jihar Jigawa da kuma wajen-ta. A nasa jawabin shugaban kwamatin, kuma babban Sakataren yada labaran Gwamnan Jiha, Malam Hamisu Muhammad yayi alkawarin yin aiki kafada da kafada da kungiyar domin karfafa aikin Jarida a Jihar Jigawa da ma kasa baki daya.