Kungiyar Miyetti Allah ta kasa reshen jihar Jigawa ta ce zata gudanar da sabon zaben shugabannin kungiyar na kananan hukumomin jihar nan 27 sakamakon karewar waaadin mulkin shugabannin
Shugaban kungiyar na jihar Jigawa, Alhaji Wada Baya ya sanar da hakan a lokacin jawabin bankwana ga shugabannin kungiyar na kananan hukumomi masu tafiya
Ya ce kundin tsarin mulkin kungiyar ya bada waadin yin shekaru hudu ga shugabannin kungiyar dan haka waadin mulkin shugabannin na kananan hukumomi ya zo karshe
Alhaji Wada Baya yana mai cewar an kira taron ne domin gode musu bisa kokarinsu na ciyar da kungiyar gaba a matakin kananan hukumomi
A jawabinsa mataimakin Odita na kungiyar na kasa Lawan Baso Mai Fulanin Gumel ya ce ya halarci taron ne domin wakiltar uwar kungiyar ta kasa
Ya kuma nuna gamsuwa da irin biyayyar shugabannin kungiyar na kananan hukumomi , inda ya ce zasu tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da sabon zabe
A nasa jawabin Uban kungiyar Miyetti Allah Alhaji Ya’u Haruna Malam Madori ya ce an shirya taron ne domin tattaunawa kan nasarori da akasin hakan domin cigaban kungiyar Ya shawarci shugabannin kungiyar da waadin su ya kare da su cigaba da yiwa kungiya hidima ta hanyar wayar da kai da kuma fadakarwa.