Honarabul Abubakar Fulata ya bayar da tallafin naira miliyan 45 ga yan jam’iyar APC na mazabar sa

0 460

Wakilin mazabar Birniwa, Guri da kuma Kirikassamma a majalissar wakilai ta kasa Honourable Abubakar Hassan Fulata ya kaddamar da bada tallafin bunkasa tattalin arziki na naira miliyan 45 ga masu ruwa da tsaki na jamiyyar APC na mazabarsa.

An kaddamar da biyan tallafin ne a karamar Hukumar Birniwa, inda aka raba naira miliyan 15 ga yan jamiyya 750 inda kowannensu ya samu naira dubu ashirin.

A jawabinsa wajen bikin, Hadimin Dan Majalissar a karamar Hukumar Birniwa,  Musa Muhammad Isyaku ya ce za a raba naira miliyan goma sha biyar biyar ga masu ruwa da tsaki na jamiyyar APC guda 750 a kowacce karamar hukuma ta dan majalissar da suka kunshi  Birniwa da Kirikasamma da kuma Guri

A cewarsa wadanda zasu amfana da tallafin sun hadar da shugabannin jam’iyya na kananan hukumomi da shugabannin mazabu dana akwatina maza da mata da kuma agent agent na jamiyya da kungiyoyi da kuma yayata manufofin jamiyya ta kafar sadarwa ta zamani

Ya ja hankalin masu amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata wajen bunƙasa sana’o’insu na yau da kullum.

A nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar APC na karamar Hukumar Birniwa, Magaji Matara, ya nuna jin daɗinsa bisa ƙoƙarin dan majalissar tarayya na ci gaba da tallafawa al’ummar mazabarsa. A jawabinsa Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jiha Alhaji Ya’u Yakubu Kanya, ya yaba da ayyukan raya kasa da Abubakar Hassan Fulata ya aiwatar a yankin Birniwa.

Leave a Reply